Wird geladen....

JAMB UTME - Hausa - 2010

Frage 1 Bericht

A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.

‘‘Ba neman aure ke da wuya ba, shigaka-fito’’. Ka ga shiga-ka-fito ɗin nan, lallai shiga-ka-fito ɗin ne! Domin aljihu kan jigata kafin a kai ga biki. Tuddan da al’ada ta tanada, waɗanda dole sai an haye su, suna da yawa.

Yanzu ɗauki misalin kayan na–gani-inaso, wato ’yan kayan nan da ake shiryawa a kai gidan su yarinya a karon farko. Ma’anar yin haka, wai iyaye su san cewa manemin auren ’yarsu da gaske yake. To, ina dole ga yin haka? Da can da yake zuwa yana zance da ’yarsu yana yi mata hasafi, ba a san da gaske yake ba?

Gangaro kan kayan toshi. Nan ma tsabagen kuɗi ake kashewa a sayi suturu da kayan shafe-shafe a kai wa yarinya. Kada fa ka ce zuwa zance da manemi yake yana yi wa yarinya kyauta mako-mako, shi ke nan, ya wadatar. Ina, ko kaɗan!

Kada ka mance da kuɗin gaisuwar iyaye da dukiyar aure kafin a yi baiko da sa ranar biki. Kuɗi ne maɗiɗɗiki ake tanada a kai wa iyayen yarinya da niyyar dai wannan abu da aka ambata.

Duk bayan wannan, ana sa ranar aure, manemin yarinya ya dosa karakaina ke nan daga wannan gida zuwa wancan, ko ma wannan gari zuwa wancan da sunan gayar da iyaye da kakanninta, wai don su san shi. I, za su san shi mana, tun da ba yana zuwa ne ziƙau ba! Da zarar biki ya kawo jiki kuma, uwa-uba za a shirya kayan lefe na fitar hankali a kai wa yarinya. Nan ma dukiya ake narkawa.

Haƙiƙa duk waɗannan abubuwa al’ada ce kawai ta ƙaƙaba wa al’umma. Ai ta fuskar dukiya, muhimmin abu ga aure, sadaki. Amma abin takaici, yanzu an yi masa mahalli a can ƙarshen sahu!

Yaushe manemin yarinya ke zuwa gayar da iyaye da kakanninta?