Loading....

JAMB UTME - Hausa - 2010

Question 1 Report

A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.

A karkara da ma wasu manyan garuruwa ƙalilan, mutane kan haɗu su riƙa cin abinci tare. Akan zaɓi gidan mutum ɗaya daga cikinsu ya zama shi ne matattara. Mutumin da aka zaɓi gidansa, kusan shi ne shugaba, kuma ya fi kowa yawan shekaru. A wasu lokuta kuma, ana duba gidan da ya fi yalwa, ko ya fi zama kan hanya, babu wahala sosai zuwa gidan, musamman da damina.

A wurin haɗuwa a ci abinci tare, kowane magidanci zai kawo abincin da aka dafa a gidansa, wanda ya fi shiga. Nan fa matan da suka ƙware suke shan yabo da godiya. Waɗanda ba su iya ba kuwa, aiki ya gan su da kuma takaici. Saboda wasu mazan kan yi wa matansu gori. Ba nan ma abin ya tsaya ba, rashin iya abincin nan na iya haddasa mutuwar aure, idan ba a kai hankali nesa ba. Al’amari ya yi muni ke nan.

Cikin abubuwan da ake kawowa, akwai tuwo da shinkafa da fate da ɗan wake da dambu da alkubus da doya da taliya da kuma makaroni. Ana kawo wasu daga cikin waɗannan nau’o’in abinci tare da miya, wasu kuma a siffar dafa-duka. Duka dai wannan, ya danganta da irin cefanen da maigida ya yi. Akwai alfanu babba game da wannan zama. Da farko, akwai kyautata dangantaka da zaman tare. Ana kuma taimakon juna ta hanyar tattauna matsalolin da suka addabe su. Wanda ma ba ya da ƙarfin yin abinci wani lokaci, ba zai tagayyara ba, zai sami abin da zai ci a wajen.

A labarin, kalmar ƙware na daidai da